Dakarun sojin Kamaru sun ce mayakan kungiyar sun kai harin ne a wani kauye da ke arewacin garin Kolofata, a ranar Alhamis da daddare.
Maharan sun tsallaka kan iyaka zuwa cikin Najeriya, kafin sojojin Kamaru su iso.
Kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a arewacin Kamaru da Chadi da kuma Nijar, amma mafi yawancin hare-harenta a Najeriya ne. ABNA